الخميس، 5 أكتوبر 2017

DUNIYA MAKARANTA


 
DUNIYA MAKARANTA
Rubutawar Dr. Mansur Sokoto
*** Urwatu bn Zubair, ya gamu da jarrabawar ciwon Cancer a kafarsa. Da magani ya gagara sai aka yanke shawara aka cire masa kafar ga baki daya. Amma a wannan dare bai fasa karanta abin da ya saba yi na Alqur'ani da Zikirin ubangiji ba. Duba ka gani, sau nawa ne karamar matsala ta durkushe ka daga ibada?
*** Kyawon hankali ya rika tunani. Kyawon harshe ya rika fadin gaskiya. Kyawon Budurwa kunya. Kyawon Yaro biyayya.
*** Idan ka kyautata ma mutum za ka mallake shi. Idan ka wadatu daga mutum za ka zama tsaran sa. Idan kuwa ka bukatu zuwa ga mutum, to dole sai ka zamo bawansa.
*** Tuntuben harshe ya fi tuntuben kafa zafi. Na kafa saurin warkewa yake yi, na harshe kuwa illanta mutum yake yi har karshen rayuwarsa.

ليست هناك تعليقات:

إرسال تعليق